Liyafar Murnar Dawowar Shugaba Buhari:  Mutane 40 suka Halarta Bana Sabanin 300 a Bara

 

Mai shirya liyafar murnar dawowar Buhari duk lokacin da yaje jinya ya ce mutum 40 suka halarta bana sabanin 300 a bara.

Wani dan a Mutanen Buhari, Abubakar Rabiu, ya shirya taron walima ta musamman don murnar dawowar shugaba kasan daga birnin Landan inda yaje hutawa ko jinya.

Da yammacin Juma’a yayin rana ta fadi kuma lokacin shan ruwa yayi, Abubakar Rabiu, ya tara jama’a a wani gidan cin abinci dake gaban jami’ar tarayya a Dutsinma, jahar Katsina.

Rabiu, wanda aka fi sani da Abu albarka, ya kasance babban masoyin shugaba Buhari kuma ya kasance yana yanka rago don walima duk lokacin da Buhari yayi tafiya ya dawo musamman na jinya.

A cewar Daily Trust, wannan shine karo na takwas da zai shirya liyafa.

Abokansa masoya Buhari sun samu halartan wannan liyafa inda suka yi addu’an Allah ya karawa shugaban kasa lafiya.

“Bana mutum 40 suka halarta don shan ruwa. Wannan shine adadi mafi karancin da muka samu, la’lla saboda azumin Ramadanda ne, bara kimanin mutum 300 suka halarta,” yace.

Abu Albarka ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari nan matukar kokari wajen magance matsalar tsaro da karfafa tattalin arziki.

Ya yi kira ga yan Najeriya su cika da addu’a ga shugabannin Najeriya don zaman lafiya da cigaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here