Kashi 95% na Kuri’un Jahar Kano a 2023 Tinubu Za’a Kadawa – Abdullahi Yanshana

 

Yayinda ake shirin murnar ranar haihuwarsa, Tinubu na cigaba da samun goyon baya.

Tun yanzu, an fara shirye-shiryen takaran zaben shugaban kasa a 2023.

Ana hasashen cewa mulki zai koma kudu bayan Buhari Shugabannin majalisun dokokin Arewa maso yammacin Najeriya sun mara goyon bayansu ga jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, don takaran kujeran shugaban kasa a 2023.

Kakakin majalisar dokokin jahar Legas, Mudashiru Obasa, ya bayyana hakan.

A jawabin da ofishin yada labaran Kakakin ya saki ranar Asabar, ya ce dukkan shugabannin majalisun sun bayyana goyon bayansu ne ranar Juma’a a jahar Kano.

A cewar jawabin, tsohon Kakakin majalisar jahar Kano, Abdullahi Yanshana, “kashi 95% na kuri’un jahar Kano a 2023 jagoran APC (Tinubu) za’a kadawa,”

Obasa ya ce dukkan shugabannin majalisun dake ci yanzu da kuma na baya a Arewa maso yamma sun alanta goyon bayansu ga Tinubu don ya gaji shugaba Buhari a 2023.

Kawo yanzu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bai bayyana niyyar takara a zaben 2023 ba.

Amma yadda makusantansa da masoyansa ke nema masa goyon baya, da alamun nan ba da dadewa ba zai alanta niyyarsa. A ranar Asabar, Tinubu ya jagorancin lakcan Arewa House karo na 11 da ya gudana a jahar Kaduna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here