Abduljabbar Nasiru Kabara Na Fama da Rashin Lafiya Har Yana Fitsarin Jini a Gidan Gyaran Hali

 

Jaridar Africa Daily News ta rawaito cewa, Abduljabbar Nasiru Kabara, Malamin nan dan asalin jahar Kano wanda gwamnatin jahar Kano ta gurfanar da shi a gaban kotu.

kuma kotun ta bada umarnin a tsare shi na fama da rashin lafiya.

Malamin wanda kotu ta bada umarnin a tsare shi ranar Juma’a bisa zargin kalaman batanci da na tunziri ya shaidawa lauyansa irin halin rashin lafiya da yake ciki wanda likitoci suka tabbatar.

A gefe guda kuma za ayiwa Malamin gwaje-gwaje kafin tabbatar da cutar dake damunsa.

Kodayake an bashi magunguna domin kula da lafiyarsa, Lauyansa, Barista Rabiu Abdullahi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a daren yau Laraba.

“Eh bashi da lafiya. Yana fama da matsanancin rashin lafiya har yana fitsarin jini.

” Likitoci sun tabbatar bashi da lafiya.”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here