Gwamna Abdullahi Sule ya Sanar da Sallamar Kwamishinoninsa

 

Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da rushe baki ɗaya masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa.

Gwamnan ya faɗi hakane a wurin taron gaggawa da ya kira a faɗar gwamnatinsa dake Lafia.

Kwamishinan shari’a ya yi jawabin godiya a madadin baki ɗaya tsofaffin ma’aikatan bisa damar da ya ba su.

Nasarawa – Gwamna Abdullahi Sule na jahar Nasarawa ya rushe majalisar zartarwa na jaharsa, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya rantsar da kwamishinonin da ya sallama ne a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2019.

Gwamnan ya sanar da wannan matakin ne yayin wani taron gaggawa na mambobin majalisar zartarwa da ya kira, wanda ya gudana a fadar gwamnatin jahar dake Lafia ranar Litinin.

Gwamna Sule ya sanar da sallamar kwamishinoni, masu bashi shawara, da manyan masu bashi shawara ta musamman banda waɗanda ke jagorantar ɓangaren ayyukan jin kai.

Sule ya yi amfani da damar da ya samu wajen gode musu bisa sadaukarwarsu wajen aiki tukuru a lokacin da suke cikin ofis a gwamnatinsa.

Tsofafin mambobin sun gode wa gwamna Da yake martani a madadin tsofaffin mambobin kwamitin zartarwa, Abdulkarim Abubakar, wanda kafin lokacin shine kwamishinan shari’a ya yi godiya ga gwamna bisa damar da ya basu a gwamnatinsa.

Ya kuma tabbatarwa gwamna Sule cewa zai cigaba da samun cikakken goyon bayansu yayin da ake fuskantar babban zaɓe a 2023.

Wane dalili yasa gwamnan ya ɗauki wannan matakin?

Wani babban jami’in gwamnatin Nasarawa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace mafiyawancin waɗanda gwamnan ya sallama sun shiga gwamnatin ne bisa shawarar magabata.

Hakan yasa ake zargin suna boye namijin kokarin da gwamnan yake yi a zamanin mulkinsa.

Yace:

“Ya zama tilas gwamna Sule ya sallamesu domin ya samu damar gina gwamnatinsa yadda yake so.”

“Matukar Sule bai ɗauki matakin da ya dace ba, to yana iya rasa tikitin takara a karo na biyu.”

“Ina da tabbacin ya yi hakane domin samun cikakken iko a gwamnatinsa yayin da yake kokarin neman zarcewa kan kujerarsa a zaɓen 2023.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here