Babban Abinda Nake Tsoro a Rayuwata – Don Jazzy

 

Fitaccen mawakin nan na zamani, Don Jazzy ya bayyana babban abun da yake tsoro a rayuwarsa.

Don Jazzy ya ce yana matukar jin tsoron wutar jahannama domin an ce idan mutum ba Kirista bane sai ya shige ta.

Ya kuma bayyana cewa idan aka duba lamarin kamar ana yi wa mutum barazana ne maimakon a bari ya bi zabinsa.

Shahararren mawakin nan na Najeriya wanda aka fi sani da Don Jazzy, ya bayyana babban abin tsoro a rayuwarsa.

Babban mawakin na kungiyar Mavin Records wanda ya yi suna wajen aikin jin kai da taimakon jama’a ya bayyana cewa “wutar jahannama ita ce babbar abin da yake tsoro”, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Don Jazzy ya bayyana wannan lokacin da ya fito a cikin shirin Nancy Isime Show.

Ya ce:

“A halin yanzu, ina tsoron Allah saboda kamar ana yi mana barazana ne da wutar jahannama.

Sun ce, idan kai ba Kirista ba ne, za ka shiga wutar jahannama.

“Kamar suna maka barazana ne. Me ya sa ba za ku bar zaɓin a buɗe ba kawai? Me yasa dole ne sai an haɗa shi da wutar jahannama? Bari in yanke shawara.

“Don haka yanzu, dole ne in gaya muku cewa ni Kirista ne saboda ina jin tsoron shiga wutar jahannama. Ina jin tsoro matuka. Wannan shine abin da na sani. Ina jin tsoron wutar jahannama.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here