Jami’ar ABU Zaria na Bukatar Tsaro – Garba Muhammad Datti

‘Yan Majalisan Kaduna sun yi magana game da rashin tsaro a yankin Zaria.

Majalisa ta bukaci a baza Jami’an tsaro, sannan a katange jami’ar ABU Zaria.

Garba Muhammad Datti ya kawo wannan kudiri a gaban Majalisar Tarayya.

A ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamba, 2020, majalisar wakilan tarayya ta koka game da matslar rashin tsaro da yake kara yaduwa a yankunan kasar nan.

Jaridar Punch ta ce majalisa ta yi wannan magana ne a dalilin hare-haren da aka kai a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da wasu makarantu a kasar.

Majalisar wakilan ta bukaci gwamnatin tarayyya, ‘ba tare da bata lokaci ba’, ta kafa katanga da zata zagaye jami’ar ABU kamar yadda aka yi a wasu jami’o’i.

Majalisar ta ce: “Akwai bukatar a hana ‘yan bindiga da sauran bata-gari shigowa cikin jami’ar.”

“Wannan majalisa tana kuma kira ga Sufeta Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ‘ba tare da wani jinkiri ba, ya kafa sansanin ‘yan sandan kwana-kwana a jami’ar, musamman a shiyyar Samaru, domin a tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin jama’a a ko da yaushe.”

“Wannan gida tana kuma kira ga shugaban hafsun sojojin kasa, Janar Tukur Buratai ba tare da bata-lokaci ba, ya kafa bataliyar sojoji a iyaka ya Kudu da jami’ar ABU, domin hana kutsowa ta wannan yanki, wanda yanzu lamari (na rashin tsaro) ya yi suna.”

Bayan haka, majalisar wakilan ta bukaci kwamitocinta na harkar ilmi da tsaro su hada-kai da IGP, hafsun sojoji da ma’aikatar ilmi domin aiwatar da abubuwan da aka fada.

‘Dan majalisa mai wakiltar Sabon-Gari, Hon. Garba Muhammad Datti ne ya gabatar da wannan kudiri a majalisa domin kare jami’ar daga miyagun ‘yan bindiga.

Sauran wadanda su ka amince da kudirin sun hada da: Tajudeen Abbas, Shehu Balarabe, Muktar Ladan da Ibrahim Hamza Muhammad, duk daga mazabun Kaduna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here