Abubuwa 4 da Nake Matukar So – Mai Martaba Nasiru Ado Bayero

 

Mai martaba sarkin Bichi, sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana abubuwa 4 da yake matukar so.

A wani bidiyo wanda aka tattauna dashi, ya bayyana yadda yake matukar son kadaici a rayuwarsa.

A cewarsa, yana matukar son karatu da tafiye- tafiye don hakan yana matukar nishadantar dashi.

Bichi, Kano – Sarkin Bichi, Mai Martaba Alhaji Nasir Ado Bayero, sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wani bidiyon tattaunawa dashi da wakilin Daily Trust ya yi ya bayyana abubuwa 4 da yake matukar sonyi a rayuwarsa.

1. Da farko ya bayyana cewa yana matukar son kadaici ba tare da wani ya dame shi ba. Yana son kadaice kansa daga cikin mutane.

Ina matukar son kasancewa ni daya saboda hakan yana bani damar yin tunani mai zurfi akan abubuwan da nayi da wadanda nake son yi a nan gaba. Saboda idan kana cikin mutane, yin tunani yana da matukar wahala don haka kasancewa kai daya zai iya baka damar samar da wani sabon abu. Ni dai ina son zama ni kadai sosai, a cewar Sarkin.

2. Sarkin ya bayyana cewa yana matukar son karatu don shi makaranci ne.

A cewarsa:

Ina matukar son yin karatu kuma ina karanta duk littafin da na samu. Ina karatu kullum, idan na kusa yin bacci akwai littafin da zan karanta,” inji Sarkin Bichi.

3. Sarkin ya bayyana yadda yake son yin tafiye-tafiye duk da dai yanzu baya iya yin tafiye-tafiyen kamar da. Amma yana matukar son ziyartar wurare iri-iri. Sarkin ya ce idan ya yi tafiyar yana son kasancewa cikin kadaici.

4. A cewar mai martata, idan ya samu lokaci yana son yin tattaki saboda ya gaji hakan a wurin mahaifinsa ne, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kasance suna yin tattaki da mahaifinsa na tsawon sa’o’i 2 zuwa uku tare, idan suka gaji sai su nemi wuri su huta su sha ruwa, tukunna sai su mike su cigaba da tafiyar.

Kuma har yanzu bai bar wannan sunnar mahaifin tasa ba, ya kasance yana yi har yanzu idan ya samu dama. A cewarsa ko jahar Legas yaje yana yin tattakin nan idan ya samu dama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here