Abubuwa 10 da Mutum ya Kamata ya sa ni Kafin ya Shiga Siyasar Najeriya – Shehu Sani
Tsohon sanata, Shehu Sani, ya zayyano wasu abubuwa har 10 da duk wani dan Najeriya zai shiryawa kafin ya shiga siyasa.
Sanata Shehu Sani ya sha kaye a babban zaɓen da ya gabata na shekarar 2019 baya hamayyarsa da gwamna El-Rufa’i ta tilasta shi barin APC.
A cewar tsohon Sanatan, jerin abubuwa 10 shawara ce ga duk wani mutum da ya neme ya ba shi kafin ya tsunduma siyasa Ga su kamar haka:
1. Kashewa shugabannin jam’iyya kuɗi domin samun tikitin takara duk da cewa babu tabbacin za su zaɓe ka. Amsa kira, halartar kowanne taron jama’a, sakarwa yan jagaliya mara da hakuri da wautarsu.
2. Takura, rashin samun lokacin kanka da na iyalanka sakamakon taro da jama’a koyaushe, ƙoƙarin haɗuwa da mutane da boyewa wasu mutanen.
3. Dole ka koyi kawar da kai daga zagi daga mutanen da kake ganin kafi ko sun fika ta kafafen watsa labaran na radiyo, tv da sauransu.
Read Also:
4. Abokan hamayyarka za su bi diddigin rayuwarka ta baya da tarihin iyayenka don samo abin suka, idan babu su kirkiro wanda za su gayawa jama’a ba. Idan ke mace ce ki shiryawa zagi kala-kala daga mazan da kika sani da waɗanda ma ba ki taɓa saninsu ba.
5. Idan namiji ne kai to addininka da asalin kakanninka duk sai an bibiya. Har makarantun da ka yi za su bi don jin mummunan halinka, in suka samu tarihin rashin lafiyarka ko mutuwar auren ka, za su yaɗata ga jama’a.
6. Ka shiryawa masu yaudara da son taɗe ka daga mutanen da kake son su, kila ma ka goyi bayansu ko ka taimakesu a wani abu.
7. Ka shiryawa shiga cin bashi don gudanar da yaƙin neman zaɓe, uwa uba sayar da kadarorinka da hannun jarinka wanda ka tara tsawon lokaci a rayuwarka, duk din ka tabbatar kana da kuɗi don tafiyar ta yi kyau.
8. Ka zama cikin shirin jin mutumin da ya ce zai taimake ka da rana ka hango shi a taron abokan hamayyarka da dare suna mitin. Ka shirya kamar ka yarda da abinda ya fada koda karya yake
9. Ka dai shiryawa shiga damuwa da tursasawa ƙwaƙwalwaka, zuciya da gangar jikinka fiye da ka’ida. Ka zauna cikin shirin jin labarai na yi maka zagon-ƙasa, barazana da rayuwarka da ta iyalanka.
10. Ka shirya bin hanya mai tsaurin gaske.