Abubuwan da Muka Fuskan ta a Hannun ‘Yan Bindiga – Daliban Afaka 5

 

An sada karin daliban biyar da suka samu kubuta da iyayensu a jahar Kaduna.

A ranar Alhamis , mun kawo muku labarin cewa yan bindiga sun sake karin 5.

Gwamnan Kaduna ya jaddada cewa ba zai yi sulhu da yan bindigan ba Daya daga cikin dalibai kashi na biyu da yan bindiga suka saki bayan sacesu da aka a makarantar ta FCFM dake Afaka, Kaduna, AbdulGaniyu Aminu, ya ce yan bindigan na hanasu Sallah kuma kullum suna bugunsu.

Bayani kan abubuwan da suka fuskanta cikin makonni uku da sukayi a daji, AbdulGaniyu ya ce bai taba shan wuya irin wannan a rayuwarsa ba.

Yayi wannan bayani ne jim kadan bayan gwamnatin jahar ta mikasu ga shugabannin makarantar. “Cikin makonni uku da na yi a daji ban yi wani baccin kwarai ba.

Ta yaya ma zakayi bacci saboda suna hanamu Sallah kuma suna zanemu tare da buga mana gindin bindiga,” yace.

A cewar Daily Trust, sunayen dalibai biyar kashi na biyu da aka sako sune Suzan Jatau, Ishaya Jafaru, Abdulganiyu Aminu, Haruna Aminu da Adamu Amin.

A jawabin kwamishana tsaro da harkokin cikin gidan jahar, Samuel Aruwan, ya yi kira ga daliban kada su yadda wannan ya karya musu gwiwa su ce zasu daina karatu.

Jiya kun ji cewa an sake sakin wasu dalibai biyar cikin 39 da aka sace a makarantar FCFM Afaka, jahar Kaduna.

Wannan ya biyo bayan mutum biyar da aka saki ranar Litinin. Adadin daliban Afaka da aka saki yanzu ya zama 10, har yanzu akwai sauran 29 hannun yan bindiga.

Yayinda Legit Hausa ta tuntubi kakakin hukumar yan sandan jahar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, yace zai yi tsokaci kan lamarin nan ba da dadewa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here