Buɗe Makaranta: Jami’ar ABU Zaria ta Saka Ranar 25 ga Watan Janairu

Daga karshe, Jami’ar ABU Zaria ta sanya ranar 25 ga watan Janairu domin buɗe makaranta.

Sai dai jami’ar ta shirya wani tsari da za ta bi wajen koyar da dalibai a wannan lokaci da ake ciki na annobar korona.

Har ila yau hukumar jami’ar ta sanar da wasu tanadi da ta shirya domin taimakawa cibiyar lafiyarta da abubuwan bukata don kare kai.

Hukumar gudanarwa ta jami’ar Ahmadu Bello University (ABU), Zaria ta sanya ranar 25 ga watan Janairu a matsayin ranar komawar dalibai makaranta.

Daraktan harkokin jama’a na jami’ar, Awwal Umar, ne ya bayyana hakan, cewa an yanke shawarar ne a taron hukumar gudanarwa ta makarantar karo na 501.

Sai dai Umar ya ce dawowar daliban zai zo a rukuni-rukuni inda dukkanin daliban dake a shekararsu ta karshe za su fada a rukunin farko, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kara da cewa: “Daliban aji daya da na aji biyu da dukkanin daliban likitanci suma za su fada a rukunin farko.Dukkanin daliban digiri na biyu za a dunga daukarsu darasi ta yanar gizo.”

Jawabin ya bayyana cewa sauran rukunin daliban za su kasance a rukuni na biyu, kamar yadda yake a kalandar makarantar.

Sai dai ya ce ranar 25 ga watan Janairun da aka sanar a matsayin ranar komawar daliban na iya sauyawa gwargwadon hali na wani umarni da ka iya fita a kowane lokaci daga bakin Gwamnatin Tarayya ko kuma Gwamnatin Jahar Kaduna.

Umar ya ce hukumar jami’ar za su yi amfani da abunda suke da shi a hannu wajen taimaka wa bangaren kiwon lafiya na makarantar da kayan kariya da kuma samar da wajen kula da duk wani rashin lafiya da ke da nasaba da korona.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here