2023: Jam’iyyar Accord ta Zabi Bello Maru a Matsayin Mataimakin Shugaban Kasa

 

Jam’iyyar Accord Party ta zabi tsohon SSG na jihar Zamfara, Bello Bala Maru matsayin mataimakin shugaban kasa.

Muhammadu Nalado, shugaban jam’iyyar Accord na kasa ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis 25 ga watan Agusta.

Farfesa Imumolen, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya yi maraba da zabin Maru, ya kuma ce yana kyautata zaton za su ci zaben 2023.

FCT Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Accord Party, Farfesa Christopher Imumolen ya zabi tsohon sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Bello Bala Maru a matsayin abokin takararsa, The Cable ta rahoto.

Sanarwar da aka raba wa manema labarai a ranar Alhamis ta ce jam’iyyar ta zabi dan siyasan daga Arewa maso Yamma ne bayan tuntuba da kuma lura da karfin fada a ji da ya ke da shi.

Da ya ke magana wurin taron, shugaban Accord Party na kasa, Muhammad Nalado, ya ce bisa dukkan alamu jam’iyyar ta yi zabi nagari da zai hada kan yan Najeriya daga kudu da arewa.

Ya bayyana gamsuwarsa cewa jam’iyyar ce za ta samar da shugaban kasa da mataimaki a Najeriya a shekarar 2023, Vanguard ta rahoto.

Ya bayyana cewa da jam’iyyar Accord ne Najeriya ta samu yanci kuma ta samar da masu kishin kasa, yana mai kira ga matasa su rungumi Farfesa Imumolen wanda matashi ne ga kuma abokin takararsa dattijo mai hikima.

Martanin dan takarar mataimakin shugaban kasar na Accord

Dan takarar mataimakin shugaban kasar, ya yi godiya bisa zabensa da aka yi a matsayin wanda ya dace da aikin.

Ya ce amince ne bayan tuntuba na lokaci mai tsawo, sannan ya fito daga jiha wacce matsalar rashin tsaro ya addabe ta.

Jawabin Farfesa Imumolen

A bangarensa, dan takarar shugaban kasar na Accord Party, Farfesa Imumolen ya ce jam’iyyarsu ce za ta lashe zaben shugaban kasa na 2023, tare da goyon bayan matasa da sauran yan Najeriya.

Ya yi maraba da abokin takararsa kuma ya ce ya dace da matsayin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here