Adadin Mutanen da ke Dauke da Kwayar Cutar HIV a Fadin Duniya

 

Wani sabon rahoto na hukumar yaki da cutar Aids ta Majalisar Dinkin Duniya, UNAids, ya nuna cewa cutuka da ke da nasaba da Aids sun rika kashe mutum daya a duk minti daya a shekarar 2021.

Haka kuma rahoton ya yi kiyasin cewa a duk minti biyu a shekarar ta 2021 budurwa daya ko matashi na kamuwa da kwayar cutar mai karya garkuwar jiki, HIV.

Rahoton wanda aka fitar a babban taron hukumar a Montreal, Canada, ya nuna cewa a fadin duniya manyan mata da ‘yan mata su ne kashi 49 cikin dari na sabbin masu kamuwa da cutar a 2021.

Amma kuma a yankin kudu da hamadar Sahara matan da ‘yan mata su ne kashi 63 cikin dari na sabbin masu kamuwar a wannan shekara.

Alkaluman sun nuna cewa akalla mutum miliyan daya da rabi ne sabbin wadanda suka kamu da kwayar cutar ta HIV.

Kazalika rahoton ya yi nuni da cewa ana samun karuwar sabbin masu kamuwa da cutar a wuraren da a da ake samun raguwa.

Duk da haka shugabar hukumar Winnie Byanyima ta ce idan aka tashi tsaye za a iya kawo karshen cutar ta Aids zuwa shekara ta 2030. rahoton ba ya yana nufin

A fadin duniya akwai mutum miliyan 38.4 da ke dauke da kwayar cutar ta HIV, kuma yankin gabashi da kudancin Afirka su ne suka fi yawan masu dauke da ita.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here