Adadin Mutane da aka Kashe a Gaza Tun Daga 7 ga Watan Oktoba

 

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce mutum 8,796 ne aka kashe a can tun bayan fara yaƙin Isra’ila da Hamas.

Hakan ya nuna ƙaruwar 271 daga adadin na ranar Talata wanda ya tsaya kan 8,525.

Ma’aikatar ta ce 3,648 daga cikin waɗanda aka kashe a Zirin Gaza ƙananan yara ne.

Isra’ila dai ta fara kai hare-hare ta sama a Gaza bayan Hamas ta ƙaddamar da munanan hare-hare a ranar 7 ga Oktoba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com