Gwamnan Jihar Adamawa ya Saka Dokar Zaman Gida a Kananan Hukumomi 2 na Jihar

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya saka dokar zaman gida a kananan hukumomi biyu na jihar.

Gwamnan ya ce gwamnati ba ta da wani zaɓi biyo bayan ƙara ruruwar wutar rikicin kabilanci a yankunan da wasu sassan.

Gombe Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce ta baza komarta ko ina a yankin don kama bara gurbin da basu kaunar zaman lafiya.

Adamawa- Domin daƙile yaduwar rikicin kabilanci da ya ƙi ya ƙi cinyewa a wasu yankunan da ke da iyaka tsakanin jihar Adamawa da Gombe, Gwamna Ahmadu Fintiri, ya sanya dokar hana fita da kananan hukumomi biyu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa dokar hana fitan ta shafi kananan hukumomin Lamurɗe da Guyuk a jihar Adamawa.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan ƙara ruruwar wutar rikici tsakanin kabilar Wajas da Lugundas a yankunan waɗan nan kananan hukumomin da wasu sassan Gombe.

Yayin nuna damuwa da takaicin kan cigaba da samun arangama tsakanin al’ummomin biyu, gwamna Fintiri ya yi gargaɗi da cewa:

“Wasu bara gurbi na kokarin kai gwamnati bango saboda haka a shirye muke mu yi duk me yuwuwa wajen kawo karshen lamarin.”

A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Humashi Wunoshikou, ya fitar ya ce:

“Mun baza komar mu ta ko ina don kama duk wasu marasa ji a yankin kuma ba mu da wani zaɓi da ya zarce mu kawo ƙarshen wannan rikicin ta kowace hanya.”

Gwamnan ya ƙara da cewa abun takaici ne da dana sani duba da abubuwan da ke faruwa, gwamnati ba ta da wani zaɓi da ya wuce ƙaƙaba dokar zaman gida.

Me dokar hana fitan da ƙunsa?

Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa gwamnati na da masaniyar wasu tsiraru na shirin ɗaukar doka a hannu ta hanyar farmakan mutane a cikin gidajen su da wuraren ayyukan su.

“Domin gudun rikicin ya wuce inda muke tsammani, mun saka dokar hana fita daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a kowace rana.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here