Zaɓen 2027: ADC ta Buƙaci Cire Shugaban INEC
Jam’iyyar adawa ta ADC a Najeriya ta buƙaci a cire shugaban hukumar zaɓen ƙasa INEC, Farfesa Joash Amupitan.
ADC ta ce hukumar ta koma ƴan amshin shatar jam’iyya mai mulki ta APC, kuma ba za ta iya amincewa da hukumar a zaɓen 2027.
Hukumar zaɓen Najeriya, INEC da ta cire sunan Sanata David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC tare da Abdulra’uf Aregbesola a matsayin sakatare janar na jam’iyyar daga na’urarta.
Read Also:
A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, INEC ta ce ta ɗauki matakin hakan ne sakamakon hukuncin kotun ƙoli da kuma shari’ar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja dangane da rikicin da ake yi tsakanin ɓangarori biyu wato David Mark da na Nafi’u Gombe.
Sai dai jagororin ADCn, a wani taron manema labarai ƙarkashin jagorancin Sanata David Mark, sun ce hankalin jam’iyyar bai kwanta da shugabancin INEC ba.
“Muna buƙatar a cire shugaban INEC ba tare da ɓata lokaci ba, da kuma sauran kwamishinonin zaɓe na ƙasa. Hukumar ba za ta iya gudanar da sahihin zaɓe ba.”
Jama’iyyar ADCn ta yi watsi da matakin da hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗauka inda ta ce za ta ci gaba da gudanar da harokokinta.
“Za mu ci gaba da gudanar da lamuran jam’iyyar mu kamar yadda muka tsara, saboda babu wata dokar da ta ce sai INEC ta halarci tarukanmu,” in ji Mark.















