Afaka: ‘Yan Bindiga Sun Sake Sakin Dalibai 5

Labarin da duminsa na nuna cewa an sake sakin wasu dalibai biyar cikin 39 da aka sace a makarantar FCFM Afaka, jahar Kaduna.

Wannan ya biyo bayan mutum biyar da aka saki ranar Litinin.

Adadin daliban Afaka da aka saki yanzu ya zama 10, har yanzu akwai sauran 29 hannun yan bindiga.

Daya daga cikin iyayen daliban ya bayyanawa TheNation cewa yan sanda sun dauki daliban a karamar hukumar Giwa.

Ya ce suna kan hanyarsu ta zuwa Kaduna yanzu haka.

Mutumin yace: “Hakan, an saki biyar cikin yaranmu. Yanzu haka muna sauraron zu iso Kaduna.”

“Ina tabbatar muku cewa yan sanda sun daukesu. Amma bamu gansu ba har yanzu.”

“Sun isowa za’a kai su asibiti domin duba lafiyarsu, amma muna jiransu tukun.”

Yayinda Legit Hausa ta tuntubi kakakin hukumar yan sanda jahar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, yace zai yi tsokaci kan lamarin nan ba da dadewa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here