Shugaban Bankin AFDB ya yi Magana Akan Yakubu Gowon

Shuganan bankin AfDB Akinwumi Adesina ya kare Yakubu Gowon kan zargin da wani dan majalisar dokokin Birtaniya yayi a kansa.

Dan majalisar ya zargi tsohon shugaban kasar a mulkin soja da sace rabin kudin CBN a lokacin da aka yi masa juyin mulki.

Sai dai Adesina, ya yi watsi da zargin, yace Gowon mutum ne mai mutunci da gaskiya.

Akinwumi Adesina, Shugaban bankin ci gaban Afrika (AfDB), ya yi martani a kan ikirarin wani dan majalisar Birtanita, Tom Tugendhat, cewa Yakubu Gowon ya sace rabin kudin babban bankin Najeriya a lokacin da aka yi masa juyin mulki a 1975.

Tugendhat, wani dan majalisar Birtaniya, ne yayi zargin a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, lokacin da suke mahawara a kan kira ga hukunta jami’an gwamnatin Najeriya kan cin zarafin mutane a zanga-zangar #EndSARS.

Legit.ng ta tattaro shugaban na AfDB ya ce, Gowon wanda ya kasance tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja ya kasance dattijo abun sha’awa mai gaskiya da mutunci.

Ya wallafa a shafin nasa: “Ku yi hankali da bayanan batarwa! Mai girma Janar Yakubu Gowon, tsohon shugaban kasar Najeriya, ya kasance mutum mai martaba sosai, kamili, gaskiya, saukin kai, karamci da mutunci.

Na san shi. Dattijon Najeriya abun sha’awa. Gaskiyarsa da mutuncinsa na da tasiri.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here