Ahmed Musa ya Bar Kungiyar Al Nassr da ke Saudi Arabia

Fitacce kuma shahararren dan wasan kwallon kafa, Ahmed Musa ya bar kungiyar Al Nassr

Kungiyar kwallon kafan da kanta ta yi wallafa hakan a shafinta na Twitter – Ta yi wa shahararren dan wasan kwallon kafan fatan alheri a rayuwarsa da sauran wasanni a gaba Fitaccen dan wasan kwallon kafa na najeriya kuma kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Ahmed Musa, ya bar kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr da ke Saudi Arabia. Musa ya bar kungiyar Al Nassr da ke kasar Saudi Arabia ne bayan kwashe shekaru 2 da yayi da kungiyar.

Kungiyar Al Nassr ta sanar da hakan a wata wallafa da tayi a shafinta na Twitter a ranar Lahadi.
Kamar yadda ta bayyana, ta yi wa fitaccen dan wasan fatan alheri. A wallafar, “Muna godiya kwararren dan wasan Najeriya Ahmed Musa, muna maka fatan alheri a nan gabba”
Dan wasan kwallon kafan mai shekaru 28 wanda ya bar kungiyar Leicester City a 2018, a halin yanzu bashi da kungiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here