Ma’aikatun Gwamnatin Najeriya da ke Daukar Aiki a Halin Yanzu
Domin karin hannaye a gudanar da ayyukansu, wasu hukumomin gwamnati na neman karin ma’aikata.
Kowace hukuma ta bayyana abubuwan da ta ke bukat, da kuma lokutan da za a rufa cike fom.
Hakazalika, bayanai da ake bukata wajen cike ayyukan sun bayyana dalla-dalla ga masu sha’awar shiga.
Ga ‘yan Najeriya masu neman aikin yi, a halin yanzu hukumomin gwamnati uku ne ke daukar ma’aikata yayin da suke neman samun karin hannaye don gudanar da ayyukansu.
Legit.ng ta tattaro muku jerin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin da suke daukar aiki a halin yanzu.
Ga su kamar haka:
1. Sojin Najeriya
Rundunar Sojin Najeriya ta fara atisayen daukar sabbin ma’aikata 82 a tsarin daukar ma’aikata na yau da kullum.
Duk cike-cike da aka tura za a tantance su ta yanar gizo, daga nan kuma za a kira wadanda suka yi nasara domin tantance su a zahiri a cibiyar kaukar ma’aikatan tsaro ta Kaduna wacce aka fi sani Ribadu Cantonment, da ke Kaduna.
Fom din neman aikin kyauta ne kuma yana nan a kafar yanar gizo ta soji wato https://recruitment.army.mil.ng. Hakazalika, za a rufe fom din a ranar Juma’a, 26 ga Nuwamba.
2. Hukumar Kula da Shaidar Mazauna Jahar Kaduna Haka kuma hukumar kula da shaidar mazauna jahar Kaduna yanzu haka tana daukar ma’aikata.
Hukumar tana kira ga wadanda suka cancanta da su nemi wadannan mukamai kamar haka:
Read Also:
Department Head – Operations
Unit Head – Admin Unit
Head – Finance
Unit Head – Inter-Agency Support
Monitoring And Evaluation Officer
Customer Service Officer
Information And Data Management Officer
Unit Head – Information And Data Management
Unit Head – Customer Service
Unit Head – Monitoring And Evaluation
Admin Officer
Finance Officer
Inter-Agency Officer
Bi wannan likau din don neman daya daga cikin ayyukan sama. Za a rufe cike fom a ranar Lahadi, 31 ga Oktoba.
3. Shirin gwamnatin Kaduna na ‘Video Stack Hackathon’
Cibiyar KADA Hive Innovation and Technology hub, wani shiri ne na gwamnatin jahar Kaduna, da ke neman mai masanin yaren na’ura kuma kwararre don habaka dandalin sadarwa na bidiyo.
Gwamnatin Nasir El-Rufai na kira ga kwararru da su samar da wani dandamali don watsa shirye-shiryen bidiyo na abubuwan cikin gida a zaman wani bangare na tsare-tsaren dabarun sa na kirkiro sabbin abubuwa a jahar Kaduna.
Baya ga ba da kwangilar kirkirar dandalin bidiyo, wanda ya ci nasara/suka ci nasarar zai/za su sami kyautar kudi N250,000.00.
Masu sha’awa za su iya shiga a matsayin kungiya ko mutum daya. Idan kuna da sha’awar, zaku iya tura bukatar hakan ta wannan likau da gwamnati ta bayar:
https://kadahivehub.com/video-stack-hackathon/?fbclid=IwAR29hXniS3EoZ6RUQ4n93vTCyxeAy-Ab_wkTFoOTagH4Ck6MBHUhAPg4zoQ
Za a rufe dauka a ranar Lahadi Oktoba, 17.