Uwargidan Shugaba Buhari, Aisha ta Roƙi a Kawo Karshen Yaƙin Sudan
Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta roƙi a a haɗa karfi da karfe domin lafar da kurar rikicin Sudan.
Read Also:
Jaridar Premium Times ta Najeriya ta rawaito Aisha Buhari na wannan kira a wani taro da ta jagoranta jiya Litinin a fadar gwamnati da ke Abuja.
A cewar jaridar Aisha Buhari na ganin akwai rawar da matan shugabannin Afirka za su iya takawa musamman wajen kai agaji Sudan.
Tun a ranar 15 ga watan Afrilu yaƙi ya ɓarke a Sudan kuma har wannan lokaci an gaggara cimma jituwar tsagaita wuta.
Sama da mutane 500 ake kyautata zaton sun rasa rayukansu kawo yanzu.