Aisha Yesufu ta Maida wa Shugaba Buhari Martani

Aisha Yesufu, ‘yar gwagwarmaya kuma jagorar zanga-zangar EndSARS, ta mayar da martani mai yaji ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya yi gargadin cewa zai magance duk wani salo na iskanci kuma ta kowacce siga aka bullo da shi.

A martanin da ta yi akan gargadin shugaba Buhari, Aisha ta ce a fadar shugaban kasa ake iskanci na gaske.

Fitacciyar ‘yar gwagwarmaya kuma daya daga cikin jagororin zanga-zangar EndSARS, Aisha Yesufu, ta mayar da martani a kan gargadin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wa ma su zanga-zanagar EndSARS a ranar Litinin.

Shugaba Buhari ya yi gargadin ne a yayin da wasu matasa su ka kara fitowa domin sake farfado da zanga-zangar EndSARS a karo na biyu a Lagos da Osun.

Buhari ya ci al washin yin maganin duk wani salon iskanci.

A cikin wani martani da ta fitar jim kadan bayan gargadin da shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na tuwita, Aisha ta bayyana shugaba Buhari a matsayin matsoraci tare da bayyana cewa a fadar shugaban kasa (Aso-Villa) ake aikata babban iskanci.

“An nemi matsoracin an rasa a lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe manoma 78 saboda kawai an kama daya daga cikinsu.

“A Aso Villa ake iskanci na gaske kuma shugaba Buhari ke jagorantarsa! kamar yadda Aisha ta wallafa a martanin da ta wallafa a kan sakon da Buhari ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here