Gwamna Sani Bello ya Umarci ‘Yan Majalisar Gwamnatinsa su Aje Mukaminsu Idan Suna Neman Kujerar Siyasa
Gwamna Abubakar Sani Bello na jahar Neja, ya umarci yan majalisar gwamnatinsa su aje mukaminsu idan suna neman kujerar siyasa.
A cewar gwamnan duk wani mai son wani muƙami a APC to wajibi ya aje aikinsa kamar yadda dokokin jam’iyya ya tanazar.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jahar, Ahmed Matane, ya fitar ranar Litinin
Niger – Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello, ya umarci masu rike da muƙaman siyasa a gwamnatinsa, waɗanda ke neman wata kujerar jam’iyya, su yi murabus daga mukamansu.
Gwamnan yace duk wanda ke da burin neman wata kujerar siyasa ƙarƙashin jam’iyyar ya gaggauta miƙa takaradar murabus ɗinsa, kamar yadda Punch ta rawaito.
Sakataren gwamnatin Neja, Ahmed Matane, shine ya bayyana saƙon gwamnan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Meyasa gwamnatin Neja ta ɗauki wannan matakin?
Sakataren ya ƙara da cewa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin yin biyayya ga dokokin jam’iyyar APC mai mulki.
Sanarwa ta ƙara da cewa duk wanda ya yanke hukunci zai iya miƙa takardar murabus dinsa ofishin sakataren gwamnatin jahar nan take.
Wani sashin sanarwar yace:
“Duk mai bukatar neman wata kujera a jam’iyya, to ya gaggauta mika takardar murabus ga ofishin sakataren gwamnati nan take.”
Daga ƙarshe, sakataren gwamnatin ya yi fatan duk wanɗanda wannan umarni ya shafa zasu gaggauta yanke hukunci da yin abinda ya dace bada jimawa ba.