Akpabio ya Buƙaci Gwamnatin Tarayya ta Soke Wasu Ma’aikatun Gwamnati

 

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio ya buƙaci gwamnatin tarayyata ta soke wasu ma’aikatun gwamnati, sannan ta yi garambawul a wasu, ta yadda za a samu ingantuwar aiki.

Yayin da yake jawabi jim-kadan kafin shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024 a zauren majalisar, Sanata Akpabio ya ce hakan zai tabbatar da an gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Shugaban Majalisar dattawan ya shawarci gwamnati ta duba hanyoyin rage basukan da ta gada daga tsahuwar gwamnati.

Sanata Akpabio ya kuma bayyana cewa majalisa za ta bai wa ɓangaren zartarwa haɗin kai domin aiwatar da kasafin kuɗin yadda ya dace.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com