Akwai Yiwuwar Gwamnoni Biyu na PDP Zasu Koma APC – Ayogu Eze

Ayogu Eze ya ce ba da dadewa ba wasu Jihohi za su koma hannun APC.

Bayan APC ta karbe Imo da Ebonyi, jam’iyyar ta na ta harin wasu jihohin.

Eze ya ce nan ba da dadewa APC za ta kara kafa wasu gwamnoni a Kudu.

Wani daga cikin manyan APC a kudancin Najeriya, Ayogu Eze, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba, jam’iyyarsu za ta samu karin wasu gwamnoni.

Jaridar The Sun ta rahoto Mista Ayogu Eze ya na cewa akwai gwamnonin jam’iyyar PDP da za su fice su sauya-sheka, su dawo cikin tafiyar APC mai mulki.

Eze wanda ya tsaya a matsayin ‘dan takarar gwamnan jihar Enugu a jam’iyyar APC ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya raba kayan bikin sabuwar shekara.

Da ya ke rabawa ‘ya ‘yan jam’iyyar ta su ta APC wadannan kaya, an rahoto Eze ya na cewa:

“Daminar jam’iyyar APC ta kusa kankama idan har kuwa mun iya wanke allonmu, za mu samu damar da za mu kafa sabuwar gwamnati a nan jihar Enugu.”

“Mu na bukatar mu kafa tubalin gini mai kyau, idan mu ka yi wannan, a shekarar 2023, jam’iyyar APC za ta kafa gwamnati.” Inji jagoran ‘yan hamayyar Enugu.

Eze ya ce yanzu APC ta na kara shiri, ta na hada-kai da sauran jam’iyyu domin ta yi nasara a 2023.

“Ina so kuma in fadu maku a madadin shugabanninmu ba mu sakakance ba, APC tana zama wata amarya a Kudu maso gabas, jihar Ebonyi ta fadi, Imo ta fadi.”

Ayogu Eze ya ce: “Ina hasashen jiha daya ko biyu za su fadi kwanan nan.” ‘Dan siyasar ya ce idan su ka dage, akwai yiwuwar Ibo su iya fito da shugaban kasa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here