Alaka da Ta’addanci: Dr Pantami Ya Gargadi Masoyansa Akan Kada Su Mai da Martani
Minista Dr Pantami ya mai da martani kan kage da wata jarida ta yi masa ta alaka da ta’addanci.
Ya gargadi masoyansa da cewa, kada su mai da martani ko hantarar wani a kan abinda ya faru.
A cewar ministan, duk wanda ya zo da wata magana da ba gaskiya ba kada a dauke ta kuma yi masa nasiha Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Ali Pantami ya bukaci masoyansa da ka da su tayar da hankali game da kage da wata jarida ta yi masa na alaka da ta’addanci.
Read Also:
A martanin da ya yi kan zargin, ya ce ka da wani daga cikin magoya bayansa su zagi wani ko su daki wani a madadinsa.
A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta gano, ministan, kuma shahararren malamin addinin Islama yana cewa;
“Duk wanda yake tare ban yarda ya zagi wani ba, ban yarda ya yi wa wani kazafi ba, ban yarda ya aibata wani ba, ban yarda ya daki wani ba, ban yarda ya yi komai ba.
“Idan mutum ya yi maganar da ka ga bai dace ba; ka yi masa nasiha.
Idan ya zo da labarin da bai dace ba ko gaba da gaba ne ko a rubuce ne kace masa ba haka bane ka gyara. Idan ya dauka fani’ima idan bai dauka ba shi da Allah.
“Ba anan zamu tabbata ba, akwai wata rayuwa bayan wannan ta duniya.”