Miyetti Allah ta yi Allah Wadai da Kashe Musulmai Matafiya 25 a Jos

 

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da kashe musulmai da wasu ‘yan ta’addan kiristoci suka yi a Jos.

Miyetti Allah ya bayyana hakan a matsayin mummunan abu, kuma ya kamata a gaggauta daukar matakin kan lamarin.

Kungiyar ta kuma yi ta’aziyya da mika jaje ga iyalan wadanda suka rasu da kuma wadanda suka raunata a harin.

Jos, Filato – Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu ‘yan ta’adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, Punch ta ruwaito.

Wasu ‘yan ta’adda a ranar Asabar sun kai hari kan jerin gwanon motocin bas da ke dauke da matafiya musulmai, inda suka kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.

Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba.

Baba Othman ya ce:

“Harin na kwanton baunar da ya faru da misalin karfe 10:00 na safe, ya kuma raunata matafiya da dama, yayin da wasu 40 kuma ba a ji duriyarsu ba.

“Matafiyan suna cikin ayarin motocin bas guda hudu, lokacin da aka kai musu hari.

“Miyetti Allah ta yi Allah wadai da wannan tashin hankali mara ma’ana akan matafiya.

“Muna kira ga hukumomin tsaro da su zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aikin kuma su gurfanar da su a gaban kuliya.”

Ngelzarma ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata.

Ya ce ba za a iya samun wanda ya yi nasara ba a tashin hankalin da ba shi da ma’ana kuma dole ne a dakatar da zub da jini.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here