Amai da Gudawa ta yi Sanadin Mutuwar Mutane 12 a Sansanin Tsoffin Mayakan Boko Haram

 

Annobar amai da gudawa ta yi sanadin mutuwar wani adadi na mazauna sansanin Shokari da aka tsugunnar da tsoffin mayakan Boko Haram da iyalansu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Shaidu sun ce a kalla mutum 12 ne suka mutu ciki har da kananan yara guda hudu sanadin cutar ta kwalara.

Sai dai hukumomi sun ce mutane kalilan ne aka ba da rahoton sun kamu da cutar.

Dubban tsoffin mayaka masu ikirarin jihadi ne daga kungiyar Boko Haram ke zaune a sansani da ke cikin jihar Borno

Da yawansu dai sun watsar da harkokin kungiyar inda suka mika kansu ga hukumomi bayan mutuwar jagoransu Abubakar Shekau a bara.

Sai dai mutanen da ke rayuwa a sansanin sun ce suna zaune ne cikin wani yanayi maras tsafta, yayin da wasu majiyoyin ke cewa masai tana ta malalar da bayan gida.

Kungiyar ba da agaji ta Médecins Sans Frontières ta ce lokaci daya an samu ‘yar karuwa ta adadin masu fama da cutar amai da gudawa a Maiduguri.

Bara, Najeriya ta yi fama da cutar kwalara mafi muni a shekarun baya-bayan nan inda mutane sama da 100,000 suka kamu kuma wasu kimanin 3,500 suka mutu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here