Ambaliyar Ruwa ta yi Sanadiyyar Kashe Mutane 7 a Koriya ta Kudu

 

Mutum bakwai sun mutu a Koriya ta Kudu bayan ambaliya ta janyo nutsewar su a wani wurin ajiye motoci na karkashin kasa.

Mutanen sun je ne domin daukar motocin su amma sai suka nutse cikin ruwa da ya cika wajen.

Jami’an ceto sun bayyana ceto mutum biyu wadanda suka tsira bayan kama wasu bututai da kuma haurawa kansu na tsawon sa’a 12.

Ambaliyar mai suna Typhoon Hinnamnor da mutane basu saba gani ba ta daidaita sassan kasar ta Koriya ta Kudu a farkon wannan mako.

Masu ceto sun yi ta dafifi kamun su samu shiga wurin da mutanen suka nutse a ranar Talata da daddare.

A cewar shafin yada labarai na Yonhap, dukkan mutane taran na zaune a wani gini ne wadda jami’ai suka baiwa umurnin dauke motocin su daga wurin tun safiyar Talata.

An ruwaito cewa wadanda aka ceton da suka hada da wani mutumi mai shekara 30 da kuma wata mata ‘yar shekara 50 na cikin koshin lafiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here