Dalilin da Yasa Muke Amfani da Otal ɗin da Muka Kwace a Hannun Sambo Dasuƙi – Hukumar EFCC

 

Hukumar dake yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta bayyana dalilin da yasa take amfani da Otal ɗin da aka kwace a hannun Sambo Dasuƙi.

Shugaban EFCC reshen jahar Kaduna ya ce jami’an su na amfani da wurin ne na ɗan wani lokaci musamman waɗanda aka canza ma wurin aiki zuwa Kaduna.

Sai dai wata ƙungiyar matasa dake Badarawa ta yi zargin cewa kayayyakin amfani na cikin Otal ɗin sun yi ɓatan dabo Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana dalilin da yasa take amfani da Otal ɗin da ta ƙwace daga hannun tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuƙi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa EFFC ta ƙwace Halal Fountain Hotel (Annex) dake lamba 29A, hanyar Rabah, jahar Kaduna daga hannun Sambo Dasuƙi.

Kwanakin baya dai, jaridar Dailytrust ta ruwaito yadda Otal ɗin da ake bincike akansa kan zargin batar dala biliyan $2.1bn kuɗin makamai wanda Sambo Dasuki ke da hannu a ciki, ya zama wurin hutun wasu daga cikin jami’an hukumar EFCC.

Shugaban hukumar EFCC reshen jihar Kaduna, Sanusi Abdullahi ya tabbatar da wasu jami’an su na amfani d Otal ɗin.

Ya ce jami’an da aka canza ma wajen aiki zuwa Kaduna na amfani da wurin a matsayin masaukin su na wani lokaci.

Sai-dai wata ƙungiyar matasan Badarawa sun bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin Otal ɗin da suka haɗa da talabishin ɗin dakunan Otal ɗin sun yi ɓatan dabo.

Amma Abdullahi ya ce ba gasƙiya bane abinda matasan suka faɗa cewa wasu kayayyakin wajen sun ɓace. Ya kuma ƙara da cewa EFCC ta yi namijin ƙoƙari wajen tabbatar kayan amfani Otal ɗin basu lalace ba.

Shugaban hukumar na jihar Kaduna ya ɗakko hotunan kayan cikin Otal ɗin don tabbatar da maganar sa cewa hukumar na amfani da wurin ne na ɗan wani lokaci.

Sai dai duk da haka wakilin jaridar Dailytrust bai tabbatar da ko kayayyakin cikin Otal ɗin nanan yadɗa suke ba, saboda sun hana shiga ɗakunan cikin Otal ɗin.

Sannan kuma kofar shiga Otal ɗin abuɗe take kuma wakilin ana hangen abuɓuwa hawa a harabar cikin sa.

Amma wani mutumi da ya fito daga cikin Otal ɗin ya bayyana cewa wurin na ƙarƙashin bincike saboda haka ba kowa ke amfani da shi ba. Muttumin ya ce:

“Jami’an EFCC da suka fito daga wajen ɗaukar horo ne kaɗai ke amfani da wajen. Kuma sunce suna amfani da shi ne na ɗan wani lokaci kafin su sami wurin zama na din-din din.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here