Amfanin Mulkin Biden

Sanata Joe Biden ne ya zama zakara a zaben shugaban kasar Amurka da aka yi ranar Talata, 3 ga wata.

Masu nazarin siyasar duniya na ganin cewa mulkin Joe Biden zai amfani Najeriya da saurn kasashen nahiyar Afrika Bayan Joe Biden ya zamanto zakaran da ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka,wani rahoto da jaridar Quartz Africa ta wallafa, ya yi hasashen yadda gwamnatin Biden zata canja alaƙar Amurka da Nahiyar Afirka bakiɗaya.

Legit.ng Hausa ta kalato muku wasu daga cikin abubuwan da rahoton ya ƙunsa.

1. Zai ƙara danƙon alaƙarsu da Afirka

Rahoton yayi nuni da cewa akwai yiwuwar Biden ya aro tunanin Trump na ganin ƙasar Sin(China)a matsayin abokiyar karawarsu a nahiyar Afirka.

Wannan zai janyo ƙasar Amurka ta ƙara mu’amala da Afirka don ganin ta zarce China.

2. Ɓunƙasa ɗaukar nauyin kuɗaɗe

Acewar rahoton wataƙila Biden zai iya aringizon biyan kuɗaɗen baya da ba’a biya don tsaren tsaren da suka shafi cigaban Afirka.

Sabuwar gwamnati mai zuwa na iya dakatar da tsarin da hana Amurka ware kuɗaɗe don yin tsare-tsaren cigaba da bunƙasawa a Afrika.

3. Goyawa Ngozi Okonjo-Iweala don ganin ta shugabanci ƙungiyar kasuwanci ta duniya(WTO)

Daga cikin yunƙurin da ake hasashen gwamnatin Biden zata yi shine marawa tsohuwar ministar kuɗin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala, baya don ganin ta ɗare kujerar shugabancin WTO.

Ngozi Okonjo-Iweala dai ta samu goyon bayan ƙasashen Turai (European union), Ƙasashen Afirka, da manyan ƙasashen Asiya irinsu Japan da china da sauransu.

Da tuni an sanar da sunanta a matsayin shugabar WTO, amma kasancewar kasar Amurka ƙarkashin shugaba Trump na goyin bayan wata ƴar takarar ya kawo cikas.

4. Shiga ƙawancen samar da rigakafin Korona.

Amurka a ƙarƙashin shugaba Trump taƙi yarda ta shiga tsarin samar da allurar rigakafin Korona (COVAX).

An ƙirƙiri tsarin ne don tabbatar da wadatuwa da rarraba alluran rigakafin yadda ya dace da zarar an samar da ita.

Biden na iya shiga tsarin idan ya karɓi gwamnati.

Idan har Amurka ta karɓi tsarin, za’a samu ƙarin kuɗaɗe wanda daga bisani ƙasashen Afirka da sauran ƙasashen duniya zasu ci moriya.

5. Zai hana Amurka janyewa daga ƙungiyar lafiya ta duniya WHO

A matsayin Amurka na ƙasar da tafi kowacce bada gudunmuwar kuɗi da taka rawa a ƙungiyar WHO, ficewarta ba ƙaramin girgiza al’amurran ƙungiyar zai yi ba.

Kuma hakan zai fi shafar nahiyar Afrika, tunda ayyukan ƙungiyar nada muhimmanci sosai a nahiyar

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here