Gwamnatin Amurka ta Kama Babban Hadimin Gwamnan Jahar Ogun, Abidemi Rufai a Kan Laifin Damfara

 

Gwamna Dapo Abiodun na jahar Ogun ya dakatar da Abidemi Rufai.

Gwamnatin Amurka ta kama Rufai, wanda ya kasance babban hadimi na musamman ga Abiodun kan ayyuka na musamman bisa zargin zamba.

Sai dai gwamnan, ya ce ba za a iya kama shi da laifin abin da Rufa’i ya aikata ba Sa’o’i kadan bayan gwamnatin Amurka ta kama shi.

Gwamna Dapo Abiodun na jahar Ogun ya dakatar da babban mataimakinsa na musamman a kan ayyuka na musamman, Abidemi Rufai.

Ofishin Bincike na FBI ya kama Rufa’i a birnin New York kan zarginsa da hannu a damfarar dala 350,000 na tallafin marasa aikin yi a ƙasar.

Yayinda yake maida martani ta bakin babban sakataren yada labaransa, Kunle Somorin, gwamna Abiodun ya ce labarin kasancewar hadiminsa da hannu a cikin zamba abun damuwa ne, jaridar The Nation ta ruwaito.

Sai dai gwamnan, ya ce ba za a ɗora masa alhakin abubuwan da babban mutum mai hankali ya aikata ba.

Ya ce:

“Mun samu labari mai matukar tayar da hankali game da kame daya daga cikin masu rike da mukaman siyasa na gwamnan, Mista Abidemi Rufai a New York kan zargin zamba a Amurka, da safiyar yau.”

PM News ta ruwaito cewa Abiodun ya kuma yi Allah wadai da duk wani abu da zai kawo nakasu ga kudirinsa na kirkirar gaskiya, rikon amana a jahar da kuma cikin shugabanci.

Ya kara da cewa har yanzu yana nan kan bakansa na gina makomar jahar, yana mai cewa ba zai lamunci masu laifi ba a gwamnatinsa ko a jahar baki daya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here