Amurka ta Sanya Takunkumin Hana Zirga-Zirga a Mashigar Hormuz Bayan Taƙaddama da Iran
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya umarci rundunar sojin ruwan ƙasar da ta sanya takunkumin hana zirga-zirga a mashigar ruwan Hormuz, bayan tattaunawar da aka yi da Iran kan shirin nukiliya da kawo ƙarshen yaƙi ta gaza.
A wata sanarwa da ya fitar a dandalin Truth Social ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, 2026, Trump ya bayyana cewa an samu ci gaba a wasu fannoni yayin tattaunawar sa’o’i 20 a Pakistan.
Sai dai ya ce ba a warware babbar matsalar da ta shafi shirin nukiliyar Iran ba.
Ya sanar da cewa rundunar sojin ruwan Amurka za ta fara hana kowane irin jirgi shiga ko fita daga mashigar Hormuz nan take.
Hakazalika, Trump ya zargi Iran da yin ƙarfafa ta hanyar karɓar harajin a hannun jiragen ruwa.
Read Also:
Ya kuma ba da umarnin fara aikin lalata nakiyoyin da aka dasa a cikin mashigar domin samar da hanyar wucewa mai aminci.
Shugaban ya yi gargaɗin cewa Amurka za ta ɗauki matakin soja mai tsauri kan duk wani ɗan Iran da ya buɗe wuta ga dakarun Amurka ko jiragen kasuwanci.
Mashigar Hormuz babbar hanya ce da ake amfani da ita wajen jigilar kusan kashi ɗaya bisa biyar na man fetur ɗin duniya.
Kuma wannan takunkumi na iya janyo tashin farashin mai da kuma taɓarɓarewar tattalin arziƙin duniya.
Trump ya nuna cewa wasu ƙasashen za su iya mara wa Amurka baya a wannan fafatawa, kodayake bai ambaci sunayensu ba.
A martaninta, rundunar dakarun juyin juya halin Musulunci ta Iran ta yi gargaɗin cewa tana da iko da mashigar, kuma duk wani abokin gaba da ya yi yunƙurin ƙalubalantarsu zai fuskanci mummunan sakamako.






