An dakatar da Paul Pogba

An dakatar da ɗan wasan tsakiya na Juventus Paul Pogba na ɗan wani lokaci bayan wani binciken lafiya ya nuna sanadarin mazantaka ya yi ƙarfi a jikinsa.

Hukumar da ke binciken kwayoyi ta Italiya ta ce an binciki Pogba ne bayan nasarar da Juventus ta samu a kan Udinese da ci 3-0 a ranar 20 ga watan Agusta.

Abisa tsautsayi aka auna lafiyar Pogba bayan kammala wasan.

Idan aka same shi da amfani da ta’ammali da kwaya, za a kore shi daga fagen wasa na tsawon shekara biyu zuwa hudu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com