Anyi Garkuwa da Wasu a Abuja

 

Rashin tsaro a babbar birnin tarayya, Abuja na kara tabarbarewa a kulla-yaumin.

A wannan karon, yan sanda ne suka sanar da batun sace wasu mutane.

Wata sanarwa daga hukumar yan sanda ya ce an yi garkuwa da mutane uku bayan jami’anta sun dakile wani yunkuri na garkuwa da mutane 19.

Wasu mutane da ake zaton yan fashi ne sun yi garkuwa da mutane uku a babbar birnin tarayya, Abuja.

Rundunar yan sandan birnin tarayya ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta gani a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba.

Sai dai sanarwar, ta bayyana cewa jami’an sun dakile wani yunkuri na garkuwa da mutane 19, amma abun bakin ciki shine yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutum uku.

A cewar sanarwar, lamarin ya afku ne a shahararriyar hanyar nan ta Pei-leilei kusa da yankin Kwali a babbar birnin tarayya, jaridar The Punch ta ruwaito.

Rundunar ta sanar da ‘yan Najeriya cewa ana nan ana kokarin ganin an ceto mutane ukun da ke a hannun yan bindigar.

Wani bangare na sanarwar ya zo kamar haka:

“Rundunar na sake ba jama’a tabbacin jajircewarta na daukar matakan yaki da laifuka a kan lokaci domin tabbatar tsaron rayuka da dukiyoyi a birnin tarayya gabannin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here