Tantance Mambobi: Jam’iyyar APC ta ɗaga Ranar Fara Rijista
Jam’iyyar APC ta sanar da dage fara rijistar sabbi da tantance soffin mambobinta.
Karshen watan Nuwamba ne APC ta sanar da cewa za ta fara aikin rijistar daga ranar 12 ga watan Disamba.
Kwamitin shirye shirye da gudanarwar jam’iyyar APC ta ɗage shirinta na rijista da sake tantance ƴan jam’iyya wanda aka tsara gudanarwa ranar Asabar, 12 ga watan Disamba.
Read Also:
Yanzu za’a gudanar da rijistar a sati na biyu na watan Junairun shekarar 2021, kamar yadda Leadership ta rawaito.
Sai dai jam’iyyar ta yi shiru akan takaimaimen kwanan watan da za’a gudanar da rijistar.
Duba da gabatowar shagulgulan bikin Kirismeti, mai kula da kwamitin ya ce wannan zai bawa Kiristoci damar yin shagulgulan bukukuwan Kirismeti tare da bawa jam’iyyar damar kammala shirye shiryen yin rijistar.
A baya, kwamitin kula da tsare – tsare na jam’iyyar APC ya ce sun ce sun kammala duk shirye-shirye don fara aiwatar da sabuwar rijista da sabunta rijistar ƴan jam’iyya daga ranar 12 ga watan Disamba.