Jam’iyyar APC ta Bukaci Wani Gwamna da ya yi Murabus

Jam’iyyar APC ta zargi Gwamna Godwin Obaseki da rashin iya mulki.

Shugaban APC, ya bukaci Gwamnan jihar ya rubuta takardar murabus.

APC ta zargi Obaseki da laftowa Gwamnatin Edo bashi da rashin tsaro Shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya a jihar Edo, Kanal David Imuse, ya fito ya yi kaca-kaca da salon mulkin gwamna Godwin Obaseki.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa David Imuse ya bukaci Mai girma gwamna Godwin Obaseki ya yi murabus, ya bar wa wani kujerar.

A ranar Lahadi, 20 ga watan Disamba, 2020, Kanal Imuse ya yi wannan kira, ya ce Godwin Obaseki bai san abin da yake yi a ofishin gwamna ba.

A cewar shugaban jam’iyyar hamayyar ta APC, dabaru sun karewa gwamnatin Obaseki a jihar Edo.

Ganin yadda bashin da ke kan gwamnatin Edo ya ke kara taruwa, jam’iyyar APC ta na ganin babu abin da ya fi irin Mista Obaseki ya ajiye mulki.

Bayan haka, jam’iyyar APC mai adawa a Edo, ta na kukan halin rashin tsaro da ake fama da shi, tare da zargin gwamnatin Obaseki da saba doka.

Hakan na zuwa ne a lokacin da ake yawan samun sace-sace da tashin-tashina tun da aka samu wasu marasa gaskiya da su ka tsere daga kurkuku.

Jaridar Premium Times ta yi yunkurin jin ta-bakin gwamnan bayan kiran da David Imuse ya yi, amma Godwin Obaseki bai amsa kiran wayarsa ba.

Tuni shugaban PDP na Edo, Chris Nehikhare ya yi wa takwaransa na jam’iyyar APC raddi, ya ce bai kamata ya rika yin irin wadannan kalamai ba.

Kwanki gwamna Godwin Obaseki ya yi wa tsohon Mai gidansa, Adams Oshiomhole gorin kudi.

Abin har ta kai Godwin Obaseki ya na bada labarin yadda su ka taimakawa Oshiomhole ya nemi kujerar gwamnan jihar Edo karkashin jam’iyyar AC.

Obaseki ya bayyana rawar da ya taka a kotu har aka karbe nasarar Oserheimen Osunbor da jam’iyyar PDP, aka ba Oshiomhole nasara a zaben Edo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here