2023: APC ta ba wa Wanda Suka shiga Jam’iyyar Damar Tsayawa Takara

 

Jam’iyyar APC ta amincewa wanda suka shiga jam’iyyar kwanan nan da wanda su ke shirin shiga tsayawa takara.

Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna ne ya bayyana haka bayan taron manema kwamitin zartarwar jam’iyyar.

Daga cikin wanda suka koma jam’iyyar akwai gwamnan Ebonyi David Umahi da Yakubu Dogara, tsohon shugaban majalisar wakilai.

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC mai mulki a ranar Talata ya janye sharadin takara ga wanda suka shiga ko suke shirin shiga jam’iyyar.

Sharadin zai bada damar tsayawa takara a duk wata kujerar mulki ba tare da la’akari da dadewa a jam’iyyar ba.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka ga majalisa bayan kammala taron kwamitin kamar yada The Punch ta ruwaito.

Ya ce, “mataki na biyu shi ne kwamitin zartarwa ya sahalewa duk wanda ya shigo jam’iyyar APC kwana kwanan nan ko wanda ya ke shirin shigowa takara.

“Da wannan mataki, sababbin yan jam’iyyar za su more yanci da jindadi zaman su cikakkun yan jam’iyya. “Za Su samu damar tsayawa takara a jam’iyyar.

Za su iya takara ba tare da bukatar sai sun dade a jam’iyya ba.”

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya na cikin wanda suka shiga jam’iyyar a baya bayan nan daga jam’iyyar PDP sai kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, shi ma ya koma jam’iyyar daga PDP.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here