Shugabannin Jam’iyyar APC na Filato Sun Nuna Goyan Bayansu ga Gwamna Lalong a Zaɓen 2023
Shugabannin jam’iyyar APC na jahar Filato sun fara shirin kaddamar da takarar gwamna Lalong a babban zaɓen 2023.
A cewarsu gwamnan yana da kwarewar siyasa wajen ɗaukaka darajar Najeriya zuwa gaba idan ya zama shugabn ƙasa.
Sun kuma bayyana cewa da sun kammala tattaunawa da kowane yanki zasu bayyana aniyarsu a fili.
Plateau – Shugabannin APC na jahar Filato sun kare kudirinsu na mara wa gwamna Lalong baya ya nemi kujera lamba ɗaya a Najeriya a zaɓen 2023 dake tafe.
Dailytrust tace Yayin gawarsu a Jos ranar Lahadi domin tattauna kudirin mara wa Lalonga baya, Shugabannin sun kuma tattauna kan rikicin dake wakana a majalisar dokokin jahar.
A taron nasu, shugabannin sun bayyana cewa Lalong yasan hanyoyin shawo kan matsalolin siyasa, hakan yasa rikicin majisar bai yi muni ba.
Meyasa suke son gwamnan ya nemi takara a 2023?
Read Also:
Da yake zantawa da manema labarai a madadin shugabannin jim kaɗan bayan taronsu, Saleh Mandung Zazzaga, yace gwamna Lalong zai ɗaga martabar ƙasar nan zuwa inda mutane basa tsammani.
A cewarsa sun yi wannan hasashen ne duba da nasarorin da ya samu na rikice-rikice da kuma yadda ya saita sabanin da ake samu na ƙabila ko addini a jahar Fitalo.
Ya ƙara da cewa duk da rikicin da ake samu nan da can, gwamnan bai yi ƙasa a guiwa ba wajen jawo kowane bangare a cikin gwamnatinsa.
Yace:
“Lalong ne yake jagorantar ƙungiyar gwamnonin Arewa, kuma mafi yawan mutaɓen wannan yanki na ma na waje na yaba wa da tsarin mulkinsa.”
Lalong yana da kwarewar da Najeriya ke bukata Zazzaga ya kara da cewa gwamna Lalong yana da duk wata kwarewar siyasa wajen ɗaukaka Najeriya zuwa babban matsayi da kuma ƙara dankon haɗin kai.
Daga ƙarshe yace sun kammala shirin mara wa takarar gwmanan baya a 2023 kuma ba da jimawa ba zasu kaddamar da ita, amma a yanzun suna tattaunawar neman shawara ne daga kowane sashin ƙasar nan.