Sauya Sheka: Jam’iyyar APC ta Samu Karin Membobi Daga PDP a Jahar Osun
Daruruwan yan babbar jam’iyyar adawa PDP sun sauya sheka zuwa APC a hukumance a jahar Osun.
Daga cikin waɗanda suka sauya shekar akwai tsohon gwamnan jahar da sauran kusoshin PDP a Osun.
Gwamna Oyetola na jahar Osun tare da shugabannin APC na jaha ne suka karbi sabbin mutanen.
Osun – Ɗaruruwan mambobin jami’iyyar hamayya PDP sun sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki APC a hukumance ranar Laraba a jahar Osun, kamar yadda leadership ta rawaito.
Gwamnan jahar Osun, Adegboyega Oyetola, shine ya karbi sabbin waɗanda suka sauya shekar tare da mai ɗakinsa da sauran shugabannin APC a jahar.
Read Also:
Manyan sanannun mutane daga cikin waɗanda suka suya shekan sun haɗa da, tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Benedict Alabi, tsohon mataimakin gwamna, sanata Iyiola Omisore.
Sauran sun haɗa da mai magana da yawun majalisar dattijai, sanata Ajibola Bashiru, da kuma shugaban jam’iyya, Gboyega Famodun.
Manyan yan siyasan sun sauya sheka zuwa APC ne ƙarkashin jagorancin tsohuwar mai bada shawara ta musamman kan tsare-tsare ga tsohon gwamna Olagunsoye Oyinlola, Funmilayo Olasheinde Mustapha.
Ko meyasa suka sauya sheka?
Mustapha, wadda tsohuwar yar majalisar dokoki ce karakashin PDP, ta jagoranci ɗaruruwan magoya bayanta daga mazaɓar Ila, ta bayyana cewa ta fice daga PDP ne saboda rikice-rikicen da ya addabe ta.
Ta kara da cewa duk jam’iyyar da ba zata iya magance damuwar cikin gida ba, to ba zata iya magance ta al’ummar jaha da ƙasa ba.
Bugu da ƙari tace nasarorin da gwamna Oyetola ya samu a cikin shekara uku kacal duk da yanayin matsalar kuɗaɗen da ake ciki sun isa su jawo hankalin mutane.