APC ta Kasu Zuwa Kungiyoyi Uku – Buba Galadima

 

Tsohon shakikin abokin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima, yace kan ‘yan APC a rabe yake.

Dan jam’iyyar PDP yace a halin yanzu APC ta kasu zuwa kungiyoyi uku kuma kowacce kungiya na so ta fitar da dan takara.

Galadima yace Allah ne ya kama su kuma zai tarwatsa su, amma da kansu a hade yake, babu shakka akwai wuya kwace mulki a hannunsu Buba Galadima, tsohon makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce akwai banbance-banbance a APC wadanda ba za a iya sasantasu.

Galadima ya sanar da hakan ne yayin wani shirin gidan talabijin na AIT a ranar Laraba.

Ya yi magana a kan yuwuwar jam’iyyar mai mulki ta tsayar da hakalinta kan dan takara daya a zaben shugaban kasa na 2023 dake tahowa.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, Galadima yace ‘yan jam’iyyar APC sun rarrabe kansu zuwa kungiyoyin da sai dan kungiyar za su goyi bayan ya zama shugaban kasa a 2023.

Ya ce ‘yan jam’iyyar hudu, biyu daga kudu, biyu daga arewa, sun dauka alwashin goyon baya.

“Jam’iyyar APC ta rabu zuwa kungiyoyi uku, a takaice kungiyoyi uku da rabi.

Bakwai, bakwai, gwamnoni biyar. Kowacce kungiyar dan kungiyarta kadai za ta goyi baya ya tsaya a matsayin dan takarar shugaban kasa,” yace. “Toh muna dai kallonsu.

Allah ne ke kama su daya bayan daya. Saboda idan da Allah ya barsu a tare, akwai matukar wuya a kwace gwamnati daga hannunsu.

Hakan ne yasa suke ta janyo jama’a tare da nisantar tsoffn magoya bayansu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here