INEC ta Sanar da Okpebholo na Jam’iyyar APC a Matsayin Wanda ya Lashe Zaben Gwamnan Edo

 

Jihar Edo – Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo.

Hukumar ta tabbatar da Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a jiya Asabar.

Edo: INEC ta fadi wanda ya lashe zabe

Baturen zabe a jihar, Farfesa Faruk Adama Kuta shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Punch.

Dan takarar gwamna a APC ya samu kuri’u har 291,667 yayin da mai bi masa daga jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 247,244.

Sai kuma dan takarar gwamnan a jam’iyyar LP, Olumide Akpata ya zama na uku inda ya samu kuri’u 22,763.

“Mr. Okpebholo bayan cika ka’idojin doka, shi ya yi nasarar lashe zaben da aka gudanar.”

– Farfesa Faruk Kuta

Yawan kananan hukumomi a jihar Edo

Jihar Edo ta kunchi kananan hukumomi 18 wanda aka raba su zuwa mazabu uku da suka hada da Edo ta Arewa da ta Kudu da kuma ta Tsakiya.

Tun asali, Edo ta Arewa ta kasance inda jam’iyyar APC ta fi karfi yayin da PDP ke rike da Edo da Kudu da ta Tsakiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here