Yayin da PDP ta ɗauko Mataimakinta Daga Kudancin ƙasar Nan, APC na Shirin ɗauko nata Daga Arewacin ƙasar

 

Nan gaba a yau ne ake sa ran jam’iyyun siyasar Najeriya za su sanar da sunayen mutanen da za su mara baya ga ‘yan takararsu na shugaban ƙasa.

Jam’iyyar APC mai mulki dai za ta ɗauko abokin tafiyar ɗan takararta ne daga yankin arewacin ƙasar, yayin da PDP za ta fitar da nata daga kudancin Najeriya.

Tuni dai jam’iyyar APGA ta fitar da abokin tafiyar ɗan takararta daga arewa ita ma Ita dai PDP ta kafa wani kwamiti don tantance mutanen da ke son mara wa ɗan takararta baya.

Sannan akwai sabuwar jam’iyyar adawa ta NNPP, da ita me ake dakon ganin wa zai mata takarar mataimakin shugaban kasa. Sai kuma jam’iyyar LP, da Peter Obi ke mata takara.

Gobe Juma’a 17 ga watan Yuni za a cike wa’adin da hukumar zabe ta shata wa jam’iyyun domin mika sunayen masu takarar mataimakin shugaban kasa.

‘Yan Najeriya dai na cigaba da rade-radin mutanen da suke ganin babu mamakin jam’iyyun su tsayar, yayinda rahotanni ke cewa har yanzu ana kan tuntuba tsakanin jiga-jigan jam’iyyun.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here