Jiga-Jigan APC 3 da za su Iya Yin Nasara a Zaben Shugaban Kasa a 2023 – Salihu Tanko Yakasai
Tsohon hadimin Gwamna Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, ya lissafa Tinubu da wasu mutum biyu a matsayin ‘yan takarar kujerar shugaban kasa a 2023 na jam’iyyar APC da ka iya nasara daga kudu maso yamma.
Yakasai ya kuma ce ya kamata yankin kudu maso yamma ya samar da wanda zai gaji shugaba Buhari a 2023, ganin irin gudunmawar da shiyyar ta bayar ga nasarar APC.
Jigon na APC ya kuma ce zai zama rashin adalci idan wani dan Arewa ya gaji Shugaba Buhari a 2023.
Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimin gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yana yankin kudu maso yamma, ba a kudu maso gabas ba.
Tsohon hadimin gwamnan ya yi ikirarin cewa shiyyar kudu maso gabas ba ta da lambar siyasa da kuma dan takarar da ke da karfi don jan kuri’u a fadin kasar a zabe mai zuwa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Yakasai ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, lokacin da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Arise.
An kori Yakasai wanda ya kasance dan APC a farkon shekarar 2021 saboda sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karuwar barazanar tsaro a kasar.
Yakasai ya lissafa wadanda za su iya tsayawa takara daga kudu maso yamma
Read Also:
1. Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo
2. Asiwaju Bola Tinubu
3. Gwamna Kayode Fayemi
Yakasai ya lissafa jiga -jigan APC, wadanda ke da ikon lashe zaben shugaban kasa mai zuwa a matsayin jagoran APC na kasa, Bola Tinubu; Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo gwamnan jahar Ekiti Kayode Fayemi.
Sai dai kuma, tsohon hadimin gwamnan na kafofin watsa labarai, ya ce ba shi da wani dan takara da ya fi so daga kudu maso yamma, Daily Post ta rawaito.
Dalilin da ya sa ya kamata dan takarar shugaban kasa na APC ya fito daga kudu maso yamma
Yakasai ya kuma bayar da hujjar cewa ya kamata dan takarar shugaban kasa na APC a 2023 ya fito daga kudu maso yamma saboda shiyyar “ta matukar” bayar da gudunmawa wajen kafa jam’iyyar mai mulki.
Ya kara da cewa kudu maso yamma shine “ya ba da mafi girman gudummawa” ga nasarar jam’iyyar da lashe zaben Buhari a 2015.
Ya ce:
“A cikin APC, ya kamata mulki ya karkata zuwa kudu har ma a kudu, ina da ra’ayin dan takarar APC ya fito daga kudu maso yamma kuma ina da dalilina na fadin hakan.”
Yakasai ya kuma ce zai zama rashin adalci ne idan wani dan arewa ya gaji shugaba Muhammadu Buhari a 2023.
Ya ce:
“Ba zai yiwu APC ta kasance a kan mulki na tsawon shekaru takwas tare da shugaban kasa dan arewa sannan wani (dan arewa) ya hau mulki ya ci gaba.Wannan zalunci ne.”