APC ta Rage Karfin Boko-Haram Zuwa “Kusan Babu Komai” – Festus Keyamo

 

Jigo a tafiyar takarar Tinubu a APC ya magantu, ya ce jam’iyyar ta tabbatar kawo karshen rashin tsaro.

Shugaba Buhari ya yiwa Najeriya alkawarin kawo karshen rashin tsaro, tare da yakar cin hanci da rashawa.

Ya zuwa yanzu dai, Najeriya na ci gaba da fuskantar hare-hare daga ‘yan ta’adda daga bangarori daban-daban.

FCT, Abuja – Kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Festus Keyamo, ya ce gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar ta rage karfin Boko-Haram zuwa “kusan babu komai.”

Keyamo, wanda kuma shi ne karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust.

Ya kuma kare ayyukan gwamnatin APC a cikin shekaru bakwai da ta yi tana mulki.

Shirin ya kuma samu halartar Daniel Bwala, mai magana da yawun tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Premium Times ta ruwaito.

Alkawarin Buhari

Da Shugaba Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa 2015, jam’iyyar APC ta yi alkawarin tabbatar da bunkasar tattalin arziki, yaki da rashin tsaro da cin hanci da rashawa domin sake dawo da kasar nan kan turba.

Duk da munanan hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa al’ummomi a wasu sassan kasar, musamman a Arewacin kasar, Keyamo ya ce gwamnati ta rage aukuwar ta’addanci sosai idan aka kwatanta da yadda kasar take a karkashin gwamnatin PDP.

Ya yi zargin cewa ‘yan adawa ne suka dauki nauyin wannan labaran da ke nuna gazawar gwamnati don bata sunan jam’iyya mai mulki.

Hakazalika, ya ce ai dama gwamnatin APC ta gaji Boko Haram a hannun PDP, kuma ya zuwa yanzu dai abubuwa sun lafa nesa ba kusa ba, kamar yadda The Cable ta kawo.

Jigon na jam’iyyar APC ya ce:

“Labarin cewa gwamnati ta gaza ya zama wata waka da kusan ‘yan adawa suka dasa a makogwaron kowa ba tare da duban cikakken abin da muka yi ba.”

“Mun gaji matsalar Boko Haram. A lokacin sun kwace kananan hukumomi sama da 14 a yankin Arewa maso Gabas tare da kafa tutocinsu.

“Mun gaji rikicin manoma da makiyaya da ke faruwa tun kafin zamanin Obasanjo. Ba a kawar da Boko Haram kwata-kwata ba amma ya ragu matuka saboda mun kulla alaka da kasashen makwabta.

“Mun rage ta’addanci zuwa kusan babu shi.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here