Jam’iyyar APC ta yi Rashin Zababbun kansiloli Biyar a Jahar Oyo

 

Ana jimamin mutuwar Kansilolin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyar a jahar Oyo.

Teslim Folarin, tsohon dan majalisar dattijai ya jajantawa majalisar dokokin jahar Oyo kan wannan rashi da tayi.

Sai dai kuma ba a bayyana abin da ya yi sanadin mutuwar kansilolin ba Mutuwar wasu mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyar a jahar Oyo ya jefa jam’iyyar cikin alhini.

A cewar Jaridar The Sun, Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya bayyana cewa mambobin jam’iyyar da suka mutu an zabe su kansiloli ne a karkashin inuwar jam’iyyar.

Teslim Folarin, wani tsohon dan majalisar dattijai ya jajantawa majalisar dokokin jahar Oyo kan wannan abun bakin cikin.

Folarin ya ce:

“Na yi matukar kaduwa da bakin ciki da jin wannan babban rashi na wasu zababbun kansiloli a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jahar Oyo.

“Zuciyata ta tausayawa majalisar, iyalan APC, mazabun da suka wakilta da kuma iyalan da suka bari.”

A cewar Peoples Gazette, tsohon dan majalisar ya ce za a tuna da marigayi ‘yan siyasar saboda gudummawar da suka bayar don daukaka talakawa.

Ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya hutar da rayukansu cikin kwanciyar hankali kuma ya ba dukkansu ƙarfin zuciyar daukar wannan rashi.

Dan siyasar bai bayyana abin da ya yi sanadin mutuwar kansilolin ba.

Daga cikin mamatan akwai:

1. Honarabul Rukayat Adejumobi daga Karamar Hukumar Itesiwaju

2. Honorabul Oluyemi Muhammad daga yankin cigaban karamar hukumar Ibadan ta kudu (LCDA).

3. Honarabul Oluwole Adesokan daga Akinyele,

4. Honourable Asimiyu Ajayi daga Ido

5. Honorabul Moruf Agbedo daga Egbeda

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here