Jam’iyyar APC ta Sanar da Ranar Taron NEC

Kakakin jam’iyyar APC, Yekini Nabena ya sanar da dage taron APC NEC.

Kamar yadda aka sanar a baya, za a yi taron ne a ranar 5 ga watan Disamba.

An mayar 8 ga watan Disamba a gidan gwamnati da ke Abuja da misalin 11 na safe.

Kakakin jam’iyyar APC, Yekini Nabena, ya saki wata takarda da yammacin Lahadi, wacce ke nuna an dage taron da aka sanar za ayi na ranar 5 ga watan Disamba.

Dama daga fadar shugaban kasa za a tsara taron, jaridar Vanguard ta ruwaito hakan. Kamar yadda takardar tazo; “An dage taron gaggawa wanda NEC ta jam’iyyar APC ta shirya zuwa ranar Talata, 8 ga watan Disamban 2020.

“Gayyatar da NEC ta jam’iyyar APC wacce sakataren tarayya na shugaban CECPC, Sanata John James Akpanudoedehe ya sanar a kan za a yi taron ya nuna an daga.Duba ga matsayin jam’iyya da kuma neman mataki na gaba da jam’iyya za ta dauka.

“Sakamakon bin dokar kare kai daga cutar COVID-19, an daga taron APC NEC. Za a yi taron da misalin karfe 11 na safe a ranar 8 ga watan Disamba a gidan gwamnati da ke Abuja”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here