APC ta Sauke Shugabannin Jam’iyyarta

 

An tsawaita wa’adin kwamitin rikon kwaryan uwar jam’iyyar APC karkashin Buni.

An sallami tsohon mataimakin Oshiomole, Hilliard Eta, wanda ya shigar da jam’iyyar kotu.

Za’a shirya taron gangamin jam’iyyar nan da watanni shida.

Majalisar zartaswa, NEC, na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sauke dukkan shugabannin jam’iyya na dukkan matakai a fadin tarayya.

Wannan ya hada da shugabannin jam’iyyar na jihohi, yankuna da kasa.

Thisday ta ruwaito cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawar majalisar ranar Talata.

El-Rufa’i ya sanar da hakan ne tare da takwarorinsa na Imo da Ondo, gwamna Hope Uzodinma, da gwamna Rotimi Akeredolu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here