APGA ta Lashe Kananan Hukumomi 16 a Zaɓen Anambra

 

Alamu na nuna cewa jam’iyyar APGA ba ta shirya tattara komatsanta ba da barin gidan gwamnatin jahar Anambra ba.

Farfesa Chukwuma Soludo ne a halin yanzu ya ke gaba bayan an bayyana sakamakon zabe a kananan hukumomi 16 na jahar.

Kamar yadda INEC ta sanar, Soludo ya na da kuri’u 99,765, Ozigbo ya na da kuri’u 44,543 sai Uba da ya ke kuri’u 48,305.

Anambra – Akwai manyan alamun da ke nuna cewa jam’iyyar All Progressives Grand Alliance ba ta da niyyar tattara komatsanta ta bar gidan gwamnatin jahar da ke Awka a jahar Anambra.

Farfesa Chukwuma Soludo, dan takarar jam’iyyar a zaben gwamnan shi ke gaba inda ya lashe zabe a kananan hukumomi sama da biyu bisa uku na jahar.

Sanata Ifeanyi Uba na jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) da Valentine Ozigbo na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi nasarar lashe kananan hukumomin daddaya.

A bangaren Sanata Andy Uba na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), har yanzu bai lashe zaben ko karamar hukuma daya ba.

Ana jiran sakamakon kananan hukumomi biyu kafin a kammala tare da sanar da sakamakon karshe. Duk da akwai kananan hukumomi 21 a jahar Anambra, hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana cewa ba a yi zabe ba a karamar hukumar Ihiala ta jahar.

A dukkan sakamakon, Soludo ya na da kuri’u 99,765 a kananan hukumomi 16 na jahar, Ozigbo ya na da kuri’u 44,543 sai Uba da ya ke kuri’u 48,305

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here