Carabao: Me ya Janyo wa Arsenal Rashin Nasara?

 

Magoya bayan Arsenal sun kwana da haushin rashin lashe Kofin Carabao, kofin da suke fatan buɗe ƙofar kakar bana da shi, yayin da ke fatan lashe kofuna huɗu a bana.

Mutane da dama sun yi tunanin cewa Arsenal ce za ta lashe kofin, kafin fara wasan duba da irin ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi a kakar wasa ta ba.

Sai dai wasan ya kasance ɗaya daga cikin wasannin da ƙungiyar ta yi rashin ƙoƙari a wannan kaka, musamman a bayan komawa hutun rabin lokaci.

Ƙungiyar Manchester City ta mamaye wasan, yayin da Arsenal ta gaza yin kataɓus.

Sakamakon wasan ya yi matuƙar ɓata wa ƴan wasan na Arsenal da magoya bayan ƙungiyar rai, musamman yadda take ƙoƙari a gasar Premier da ta Zakarun Turai.

Me ya janyo wa Arsenal rashin nasara?

Matsala ta farko da Arsenal ta samu shi ne amfani da Kepa Arrizabalaga, maimakon David Raya a cewar masu bibiyar ƙwallon ƙafa.

An ci ƙwallo ta farko da ta biyu ne sakamakon kura-kuran da golan na Arsenal ya yi a wasan.

Rashin kama ƙwallon da aka bugo ya sa ɗan wasan City, Nico O’Reilly ya zura ƙwallon farko a wasan.

Haka kuma ƴan wasan Arsenal sun kasa riƙe ƙwallo a zagaye na biyu na wasan, lamarin da ya sa Man City ta jefa musu ƙwallaye har biyu tare da daƙushe fatansu.

Sannan akwai rashin manyan ƴanwasan ƙungiyar biyu, Eberechi Eze da Martin Odegaardda ke fana da jinya.

Rashin waɗannan ƴanwasa ya shafi tsakiyar Arsenal matuƙa gaya.

Duk da ƙwararrun ƴan wasan baya da ƙungiyar ta yi amfani da su a wasan, waɗanda kuma suka yi ƙoƙari, amma ragowar ƴan wasan irinsu Saka da Haverts da Rice da kuma Zubimendi, duk ɓacewa suka yi a wasan.

Sun kasa riƙe ƙwallon, kuma a zagaye na biyu na wasan, jikinsu ya nuna cewa tamkar sun gaji.

Wani abu da ya janyo wa Arsenal matsala a wasan shi ne tsarin da City ta yi amfani da shi a wasan na 4-2-4, wanda ya ba ta damar yawaita kai hare-hare zuwa gidan Arsenal da kuma hana Arsenal kai mata hari.

Ƙarfin Arsenal na ɓangren masu tsaron bayanta.

Amma buɗewar tsakiyar kungiyar ne ya janyo mata ɓaraka.

Declan Rice ya kasa taɓuka abin kirki a wasan, lamarin da ya shafi ƙoƙarin Zubimendi, kuma rashin ƙoƙarinsa ya sa Kai Havertz da Saka da Viktor Gyökeres duk suka ɓace a wasan.Arsenal da kuma hana Arsenal kai mata hari.

Ƙarfin Arsenal na ɓangren masu tsaron bayanta.

Amma buɗewar tsakiyar kungiyar ne ya janyo mata ɓaraka.

Declan Rice ya kasa taɓuka abin kirki a wasan, lamarin da ya shafi ƙoƙarin Zubimendi, kuma rashin ƙoƙarinsa ya sa Kai Havertz da Saka da Viktor Gyökeres duk suka ɓace a wasan.

Me ya rage wa Arsenal nan gaba?

Duk da rashin nasarar lashe Kofin Carabao, har yanzu Arsenal na da damar lashe kofuna uku a wannan kaka.

Yanzu haka ƙungiyar ce ta ɗaya a kan teburin Gasar Premier da tazarar mai tara, kuma za ta buga zagayen kwata fayinal ”mai sauki” a Gasar zakarun Turai da Sporting CP.

Haka ma za ta kara da Southampton a zagayen kwata fayinal na Gasar FA.

To sai dai rashin nasarar lashe Kofin Carabao ka iya yin tasiri da sanyaya wa ƙungiyar gwiwa.

Sannan kuma ko shakka babu, jinyar Eberechi Eze da Martin Ødegaard zai shafi ƙoƙarin ƙungiyar.

Arteta ya dage cewa dole ne ƙungiyar ta ɗauki wannan rashin nasara a matsayin abin da zai ƙara mata ƙarfin gwiwa.

“Za mu yi amfani da wannan baƙin ciki, domin samun ƙarin nasarori nan da wata biyu masu zuwa,” in ji shi.

A yanzu matakin da Arsenal za ta ɗauka a bayyane yake, ta koya daga kuskurenta na Wembley.

Amma masu sharhi na gargaɗin cewa idan ta buga irin salon wasan da suka buga ranar Lahadi, to za ta sha mamaki.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here