‘Dan Sanda Mai Mukamin ASP na Fuskantar Cin Zarafi a Gurin Jama’a
‘Dan sanda da mai abun hawa yaci zarafi, ASP Sunday Erhabor yace bai taba harin kowa ba ashekaru 29 da yayi yana aiki.
Dan sandan mai hakuri, yayi suna ne bayan wani bidiyonsa da ya yadu inda mai abun hawa ya ci masa mutunci a kan titi duk da yana da bindiga.
Erhabor yace yana fuskantar cin zarafi daga jama’a amma bai taba tunanin amfani da bindigarsa ba a cikin wannan hali.
Sunday Erhabor, dan sanda mai mukamin ASP, wanda wani mai abun hawa yaci zarafi a jahar Legas, yace bai taba harbin kowa ba tunda ya shiga aikin dan sanda a shekarar 1992.
Bidiyon yadda wani mutum da ‘yan sandan runduna ta musamman suka tsayar, amma ya ci zarafin ‘yan sandan ya fada kafafen sada zumuntar zamani.
Read Also:
An ga direban mai suna Victor Ebhomenyen, yana ture Erhabor, wanda ke dauke da bindiga kirar AK-47, a kirji yayin da yake yunkurin kai shi kasa, TheCable ta ruwaito.
A wata tattaunawa da aka yi da Erhabor, yace yana fuskantar tsageranci daga jama’a amma bai taba tunanin yin amfani da bindigarsa ba a irin wadannan lokutan.
“Na shiga aikin dan sanda a ranar 1 ga watan Yunin 1992.
Ina da sauran shekaru 5 kafin in yi murabus.
Ubangiji ne yake taimakona a wannan aikin,” yace.
“Wani abu ya faru a lokacin da nake FESTAC.
Ina aikin duba ababen hawa a kan hanyar Okota. Na tsayar da mota dauke da miji da matsa.
Matar ta sauko, ta wanke ni da mari.
“Nayi shiru yayin da take tambaya a kan mene na tsaresu. Kai tsaye na nufi wurin mutumin inda na tambayeshi ko shine mijin matar, yace eh.
“Sai na sanar dashi cewa matar shi ta mare ni, amma ina son ta mare shi idan har ya cika namiji.
Wannan na daya daga cikin arangamata da jama’a.
“Na fuskanci cin zarafi daban-daban, amma na kan kwantar da hankalina kuma bana sauke fushina a kan jama’a,” ya bada labari.